(ABNA24.com) A wani hari da jirgin sama maras matuki mallakin Amurka ya kai a kasar Somaliya ya yi sanadiyyar kashe fararen hula shida kamar yadda wani dan majalisar kasar ya bayyana.
Mahad Dhore ya kara da cewa jirgin na Amurka ya kai hari ne akan wata karamar motar safa da kashe mutanen da su ke cikinta da su ka hada da wani yaro dan shekaru 13 mai suna Abdulfattah, Farham Mahmud.
Dan majalisar ya kuma ce; Tuni an rufe mutanen a kusa da inda aka kashe su, saboda ba za a iya daukar gawawwakin nasu ba zuwa nesa da wurin domin sun kone
Tun da fari Amurka ta bakin sojojinta da ke Afirka ta riya kai hari ne akan wadanda ta kira; ‘yan ta’adda biyar a kusa da garin Janaale.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon dai ta tsananta kai hare-hare ne a kasar ta Somalia bisa umarnin shugaban kasar Donald Trump a 2017.
/129
14 Maris 2020 - 06:11
Lambar labari: 1017165
A wani hari da jirgin sama maras matuki mallakin Amurka ya kai a kasar Somaliya ya yi sanadiyyar kashe fararen hula shida kamar yadda wani dan majalisar kasar ya bayyana.